Mace ta hau dokin zuciya: Cacar baki ta kai wata buudurwa ga halaka yayanta a gidansu

Mace ta hau dokin zuciya: Cacar baki ta kai wata buudurwa ga halaka yayanta a gidansu

Wata budurwa yar shekaru 24, Olamide Akinbola ta bayyana ma wata Kotun majistri dake garin Ebute Meta na jahar Legas cewa bata niyyar kashe yayanta, amma bacin rai da fushi ne suka tunzura ta, kamar yadda jaridar daily trust ta ruwaito.

Dansanda mai shigar da kara ne ya fara bayyana ma Kotun cewa kimanin sati uku da suka gabata ne Akinbola ta caccaka ma yayannata wuka a gidansu dake totom Olupebi Abijo, unguwar Ikorodu jahar Legas, a lokacin da suka kaure da musu da cacar baki.

KU KARANTA: Wata budurwa yar bindiga ta bindige mutane 3 har lahira, ta kashe kanta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Akinbola cikin sanyin murya da zubar da hawaye tana shaida ma Kotun cewa ta aikata laifin ne cikin fushi: “Yayana ne, uwarmu daya ubanmu daya, na dauki fushi ne, don kuwa ban san lokacin da na kasheshi ba.”

Sufeta K.Onishakin ya bayyana a gaban Kotu cewa cacar baki ya kaure tsakanin Akinbola da yayanta, ana cikin haka sai kawai ta nufa dakin girke girke inda ta dauko wuka ta dumfari yayannat da shi, ba tare da wata wata ba ta luma masa a wuya.

Dansandan yace ganin haka jama’an dake wajen suka dauki Yayannata suka garzaya da shi zuwa Asbiti, sai dai ko kafin likitoci su fara duba shi tuni yace ga garinku nan.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkalin kotun A.O Komolafe ta bada umarnin a garkame mata Akinbola a gidan yari har zuwa ranar 28 ga watan Satumba don cigaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel