Rikici a PDP yayin da amintattun jam'iyya ke bayyana goyan bayan su ga wasu 'yan takara na jam'iyyar

Rikici a PDP yayin da amintattun jam'iyya ke bayyana goyan bayan su ga wasu 'yan takara na jam'iyyar

Mun samu cewa rikici na neman ballewa cikin jam'iyyar PDP a yayin da wasu mambobi na kwamitin amintattu na jam'iyyar ke bayyana goyan bayansu a fili ga wasu manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar.

Kwamitin yayin wata ganawa da ta gudanaa a makon da ya gabata, ya umarci mambobinsa kan hana su bayyana goyon bayansu a fili ko a boye ga kowane daya daga cikin manema takarar kujerar shugaban kasa 13 na jam'iyyar.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, jagoran kwamitin, Sanata Walid Jibrin, wanda ya tabbatar da hakan bayan ganawar kwamitin ya bayyana cewa, dole kowane mamba na kwamitin ya kiyaye ka'idoji da kuma dokoki wajen tantance ababen da suka dace da kuma wadanda ba su dace ba cikin jam'iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa, goyon bayan kowane dan takara a fili ko a bayyane na amintattun jam'iyya ya sabawa ka'idoji da kuma kundin tsarin dimokuradiyya na kowace jam'iyya a kasar nan.

Rikici a PDP yayin da amintattun jam'iyya ke bayyana goyan bayan su ga wasu 'yan takara na jam'iyyar

Rikici a PDP yayin da amintattun jam'iyya ke bayyana goyan bayan su ga wasu 'yan takara na jam'iyyar
Source: Depositphotos

Binciken da manema labarai na jaridar The Punch suka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, rikici a jam'iyyar ta PDP na neman kunno kai a yayin da wasu mambobi 3 na kwamitin amintattun jam'iyyar suka halarci bikin kaddamar da kudirin daya daga cikin manema takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar.

KARANTA KUMA: Rai 1 ya salwanta yayin da 'Yan Shi'a suka yi arangama da Sojoji a jihar Yobe

Mambobin kwamitin da suka halarci wannan biki sun hadar da; John Nwodo, Vincent Ogbulafor, wanda ya kasance tsohon shugaban jam'iyyar na kasa kuma tsohon Ministan harkokin kasashen ketare, da kuma Cif Tom Ikimi.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyyar ta PDP ta kayyade ranakun 5 da kuma 6 ga watan gobe, inda za ta gudanar da zaben fidda gwani kan takarar kujerar shugaban kasa a birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel