Nigerian Air: Ra’ayoyin jama’a bayan an fasa kafa kamfanin jirgin sama

Nigerian Air: Ra’ayoyin jama’a bayan an fasa kafa kamfanin jirgin sama

- Jama'a sun tofa albarkacin bakin su bayan an dakatar da shirin Nigerian Air

- Minista Sirika ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta fasa kafa kamfanin

Nigerian Air: Ra’ayoyin jama’a bayan an fasa kafa kamfanin jirgin sama

Najeriya ta fasa kafa kamfanin jirgin sama kamar yadda ta shirya a baya
Source: Twitter

Mun kawo maku ra’ayoyin jama’a dabam-dabam bayan da aka ji kwatsam Gwamnati ta dakatar da shirin kafa kamfanin jirgin saman Najeriya mai suna Nigerian Air. Da-dama dai wannan labari sam bai yi masu dadi ba.

Ga kadan daga cikin irin korafin da jama’a ke yi:

Irin su Gwamna Ibrahim Dankwambo dai ya soki wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka. Shi ma Aminu Tambuwal yace Gwamnatin Buhari yayi facali da sama da Biliyan 1 wajen wannan yunkurin amma duk a banza.

Ministar harkokin jirgin sama Hadi Sirika ya fito ya bayyana cewa an dakatar da shirin Nigerian Air har sai wani lokaci. Sirika ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita wanda hakan ya jawo surutai ko ta ina a Kasar.

Irin su Gwamna Ibrahim Dankwambo dai ya soki wannan mataki da Gwamnatin Tarayya ta dauka. Shi ma Aminu Tambuwal yace Gwamnatin Buhari yayi facali da sama da Biliyan 1 wajen wannan yunkurin amma duk a banza.

KU KARANTA: Buhari ya ce ka da kowa ya kula Bukola Saraki

Ministan dai bai bayyana wani dalilin kwarai wajen daukar wannan mataki ba. Ba mamaki dai Gwamnati ta lura cewa zai yi wahala shirin ya kai labari ne don haka ta dakatar tun kafin ayi nisa bayan an gama fadawa Duniya.

Dama dai can wata Ministar kasar a lokacin Shugaban kasa Olusegun Obasanjo tace babu inda wannan shiri zai kai, sai dai a lokacin jama’a sun ta dirka mata zagi da soke-soke iri-iri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel