Kwankwaso ya kamanta APC ta yanzu da PDP a 2015

Kwankwaso ya kamanta APC ta yanzu da PDP a 2015

Daya daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jam'iyyar APC mai mulki ta shiga giyan mulkin da PDP da shiga kafin zaben 2015.

A hirar da akayi da shi a shirin Sunrise Daily a Channels Tv, Kwankwaso ya bayyana cewa shi da wasu 'yan siyasa sun fice a PDP ne a 2015 saboda girman kai da daure wa masu aikata laifi gindi da jam'iyyar rika yi a wannan lokacin.

Sanatan mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya ya ce ya koma jam'iyyar PDP ne a watan Yulin wannan shekarar saboda jam'iyyar ta gane kurakurenta kuma ta gyara halayenta.

Kwankwaso ya kamanta APC ta yanzu da PDP a 2015

Kwankwaso ya kamanta APC ta yanzu da PDP a 2015
Source: Depositphotos

Ya kuma ce ya yi tsamanin zai iya cimma manufofinsa na siyasa a jam'iyyar APC mai mulki amma daga baya sai ya fahimci har yanzu APC ba ta koyi darasi ba.

DUBA WANNAN: Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

A cewarsa, a halin yanzu jam'iyyar APC ta kama hanyar girman kai da daure wa karya gindi kamar yadda PDP tayi shekaru uku da suka gabata.

"A ra'ayina PDP ta koyi darasi. A 2015, PDP tayi tunanin za ta lashe zabe ta kowanne hali. Ba ta taba tsamanin shugaba mai ci zai iya fadi zabe ba," inji Kwankwaso.

"A lokacin, PDP tana da wasu matsaloli da wasu daga cikin mu bamu amince da hakan ba, hakan yasa muka sauya sheka zuwa APC. Mun kafa jam'iyya, mun baza dukkan sassan kasar nan domin janyo hankalin mutane kuma daga baya mu kayi nasara a zaben.

"Sai dai abin takaici a yanzu, APC bata koyi darasi daga abinda ya faru da PDP ba, ba su fahimta ba kuma basu son su fahimci yadda APC na yanzu ke kamanceceniya da PDP ta 2015 kuma yanzu PDP itace APC na 2015. inji Kwankwaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel