An kai wanda ke wa dalibai fyade da wayo a badaki kotu, bayan yayi wa daliba mai tabin hankali

An kai wanda ke wa dalibai fyade da wayo a badaki kotu, bayan yayi wa daliba mai tabin hankali

- Makarantar an kafa ta ne don taimakon masu Down's Syndrome

- Masu irin matsalar kwakwalwar, basu fiye wayau ba komai girman su

- Shi malami ne a makarantar, kuma a bandaki wai yayi aika-aikar

An kai wanda ke wa dalibai fyade da wayo a badaki kotu, bayan yayi wa daliba mai tabin hankali

An kai wanda ke wa dalibai fyade da wayo a badaki kotu, bayan yayi wa daliba mai tabin hankali
Source: Depositphotos

Mista Wasu Kabiru, Malami a makarantar masu fama da cutar kwakwalwa ta Down's Syndrome, ya yaudari wata daliba da shekarunta basu fi 17 ba, inda yayi lalata da ita a bandakin makaranta, sannan bayan an kwan biyu ya kaita gida nai ya ci gaba da kowa mata badala, kotu ta saurara a yau.

Su dai masu fama da irin wannan cutar, basu fiye wayau ba, kuma kwakwalwarsu kan dauki lokaci kafin ta fahimci abu, matsala da aka fi dangana wa da kwayoyin halitta.

Down's Syndrome, takan bar babba da kwakwalwar yaro ne, kuma shi yasa ake ware su a basu makarantarsu daban domin a kula da yawan bukatunsu.

DUBA WANNAN: An karyata batun ko ana bin 9mobile biliyoyi na bashi

Wanda ake zargi, Wasiu, 29, ya musanta lamarin inda yace sam shi bai aikata fyade ba, kuma bai yii ba daidai ba da dalibar tasa.

Idan aka same shi da wannan laifi, zai rasa aiki nai, kuma yayi zaman gidan kaso na akalla shekaru bakwai babu sassaucin taara.

Ana yawan samun matsalolin fyade musamman kan kananan yara, mata da maza, a Najeriya, saboda babu wani tsari na kula da masu gigitacciyar sha'awa ko tarbiya ta kai-da-kai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel