Zaben Osun: INEC ta rarraba kayayyakin zabe yayinda aka tsaurara matakan tsaro

Zaben Osun: INEC ta rarraba kayayyakin zabe yayinda aka tsaurara matakan tsaro

Rundunar yan sanda sun tsaurara matakan tsaro kewaye da hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta dake Osogbo gabannin zaben gwamna da za’a gudanar a ranar Asabar, 22 ga watan Satumba a jihar.

An zuba jami’an tsaro da yawa a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba yayinda hukumar ta fara rabon kayayyakin zabe ga ofishoshin INEC dake kananan hukumomi 30 na jihar.

Kwamishinan zabe na jihar Osun, Mista Olusegun Agbaje ya fadama majiyarmu akan wayar tarho cewa an raba kayayyakin zabe ga kananan hukumomi a shirin gabatar da zaben ranar Asabar.

Zaben Osun: INEC ta rarraba kayayyakin zabe yayinda aka tsaurara matakan tsaro

Zaben Osun: INEC ta rarraba kayayyakin zabe yayinda aka tsaurara matakan tsaro
Source: Depositphotos

Jami’an tsaro sun rarraba junansu a kewaye da ginin hukumar INEC domin guje ma kawo kowani irin hari a ginin.

A wani lamari na daban, mun ji cewa rikice-rikice na ci gaba da samun zama a jihohin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke mulki inda gwamnoni suka samu ikon yin zaben fidda gwani na amfani da wakilai wanda hakan ya sha ban-ban da ra’ayin wasu mambobi da suke ganin za’a yi masu yankan baya.

KU KARANTA KUMA: Ranar Ashura: ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wasu ‘Yan Shi’a

A yanzu Gwamnoni sun samu goyon bayan yin amfani da zaben fidda gwani na wakilai wanda wasu kalilan ke so ayi amfani da tsarin kato-bayan-kato a daidai lokacin da jam’iyyar zata fara zaben fitar da gwaninta inda za’a farad a na shugaban kasa a ranar 25 ga watan Satumba sannan na gwamnoni ya biyo baya a ranar 29 ga watan Satumba.

Gwamnonin APC din sun yi wata ganawa a yammacin ranar Laraba, 19 ga watan Satumba, inda suka yi alkawarin marawa shugaban jam’iyyar baya domin tabbatar da zaben fidda gwani na gaskiya da amana tare da fitar da yan takaransu na zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel