APC na matakin karshe a kokarinta na kawo karshen rikice-rikice a jihohi

APC na matakin karshe a kokarinta na kawo karshen rikice-rikice a jihohi

Rikice-rikice na ci gaba da samun zama a jihohin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ke mulki inda gwamnoni suka samu ikon yin zaben fidda gwani na amfani da wakilai wanda hakan ya sha ban-ban da ra’ayin wasu mambobi da suke ganin za’a yi masu yankan baya.

A yanzu Gwamnoni sun samu goyon bayan yin amfani da zaben fidda gwani na wakilai wanda wasu kalilan ke so ayi amfani da tsarin kato-bayan-kato a daidai lokacin da jam’iyyar zata fara zaben fitar da gwaninta inda za’a farad a na shugaban kasa a ranar 25 ga watan Satumba sannan na gwamnoni ya biyo baya a ranar 29 ga watan Satumba.

Gwamnonin APC din sun yi wata ganawa a yammacin ranar Laraba, 19 ga watan Satumba, inda suka yi alkawarin marawa shugaban jam’iyyar baya domin tabbatar da zaben fidda gwani na gaskiya da amana tare da fitar da yan takaransu na zaben 2019.

APC na matakin karshe a kokarinta na kawo karshen rikice-rikice a jihohi

APC na matakin karshe a kokarinta na kawo karshen rikice-rikice a jihohi
Source: Facebook

Amma dai wasu majiyoyi abun dogaro sunce alkawarin zabe na aamanar da gwamnonin suka yin a zuwa ne bayan sun samu jajircewar shugaban APC, Adams Oshiomhole, ta yadda za’a bari su gudanar da zaben fidda gwani daban-daban ta zaben wakilai.

KU KARANTA KUMA: Ranar Ashura: ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wasu ‘Yan Shi’a

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo kuma shugaban gwamnonin APC, wanda yayi Magana a madadin abokan aikinsa a karshen ganawar ya bayyana cewa sun tattauna kan tsarin zaben fidda gwamni da za’ayi amfani dashi wajen zaben yan takarar jam’iyyar a dukkanin mukamai a zaben 2019.

Okorocha ya ce mafi akasarin jihohin APC sun yanke shawarar amfani da zaben fidda gwani na wakilai wajen zabar yan takaransu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel