Boko Haram sun kai hari 'Kauyuka 3, rayuka 6 sun salwanta a jihar Borno

Boko Haram sun kai hari 'Kauyuka 3, rayuka 6 sun salwanta a jihar Borno

Tamkar ruwan dare dangane da rahotannin aukuwar hare-haren 'yan ta'adda na Boko Haram a kasar nan, mun samu cewa kungiyar ta sake kai wani mummunan hari cikin wasu 'kauyuka 3 inda suka salwantar da rayukan mutane uku a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan ta'addan sun kai wannan mummunan hari ne ta hanyar babbake wasu kauyuka 3 dake bayan gari a birnin na Maiduguri.

Boko Haram sun kai hari 'Kauyuka 3, rayuka 6 sun salwanta a jihar Borno

Boko Haram sun kai hari 'Kauyuka 3, rayuka 6 sun salwanta a jihar Borno
Source: Twitter

Shugaban kungiyar bayar da agajin gaggawa ta NEMA reshen Arewa maso Gabashin kasar nan, Bashir Garga, shine ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mummunan lamari.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ta ruwaito, harin ya auku ne cikin kauyukan Wanori, Kaleri da kuma Konduga wanda dukkaninsu ke karkashin karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

KARANTA KUMA: Buhari ba ya da hangen nesa da zai iya ciyar da Najeriya gaba - Saraki

Legit.ng ta fahimci cewa, harin ya auku ne da misalin karfe 9.00 na daren ranar Larabar da ta gabata, inda bayan babbake kauyukan sun kuma bude wuta ta harsashin bindiga kan mai uwa da wabi.

Kazalika, wannan mummunan hari ya salwantar da rayukan mutane 6 tare kone kimanin gidaje 180 kamar yadda shugaban kungiyar ta NEMA ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel