Jam’iyyar APC ta dauki karen-tsana ta daura mana don haka na dawo PDP - Dogara

Jam’iyyar APC ta dauki karen-tsana ta daura mana don haka na dawo PDP - Dogara

A halin yanzu, Jam’iyyar APC mai mulki ta rasa gaba daya shugabancin Majalisun Tarayyar Najeriya bayan da Shugaban Majalisar Wakilai na kasar Rt. Hon. Yakubu Dogara ya koma PDP.

Jam’iyyar APC ta dauki karen-tsana ta daura mana don haka na dawo PDP - Dogara

Yakubu Dogara ya bayyana dalilin ficewar sa daga APC
Source: Facebook

Shugaban Majalisar Tarayyar ya bayyanawa manema labarai wannan ne lokacin da ya hallara Hedikwatar PDP lokacin da ya mika fam din sa na tsayawa takarar Majalisa mai wakiltar Mazabar Bogoro/Dasss da kuma Tafawa-Balewa.

Yakubu Dogara yace tun da ya shiga APC ake yi masu gorin cewa daga PDP su ka fito har a kan ce tsofaffin ‘Yan PDP ne su ka jawowa APC matsala. Dogara yace ya bar Jam’iyyar ta su don haka ya huta da jin irin wadannan maganganu.

KU KARANTA: APC ta rasa shugabancin Majalisun Najeriya bayan Dogara ya tsere

Dogara wanda ya nuna cewa yanzu ya huta da ya bar APC ya kuma dawo gida watau PDP ganin yadda aka dauki karen-tsana aka daura masu a APC. Dogara yace ba rashin tikiti da bai samu bane a APC ta sa shi ya dawo Jam’iyyar PDP.

Shugaban Majalisar yace zai nunawa masu karyar za su masa ritaya daga siyasa iyakar sa inda yace halin da Bauchi ta shiga a APC ya zaburar da shi ya sauya-sheka. Dogara dai yace nan gaba zai yi cikakken bayanin abin da faru a APC.

Yakubu Dogara ya tsere daga APC zuwa Jam'iyyar PDP ne bayan da wasu ‘Yan Mazabar sa ta Bogoro/Dass/Tafawa Balewa su ka saya masa fam din takara a karkashin Jam’iyyar PDP kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel