Prince Momoh: Tsananin kiyayyar Obasanjo ba za ta hana Buhari yin tazarce a 2019 ba

Prince Momoh: Tsananin kiyayyar Obasanjo ba za ta hana Buhari yin tazarce a 2019 ba

- Prince Momoh, ya ce duk da irin tuggu da makarcin Obasanjo ba zai samu nasara wajen hana tazarcen Buhari ba

- Ya ce musamman yan Arewa ba za su saurari Obasanjo ba ko da kuwa ya bukace su da su zabi wata jam'iyyar banda APC

- Prince Momoh ya kuma ce suna nan suna jiran yadda ADC za ta samu nasara tunda dai ita ce jam'iyyar da Obasanjo ya ke goyon baya

Prince Tony Momoh, tsohon Ministan watsa labarai, a ranar Alhamis ya bayyana cewa duk da irin tuggu da makarcin Obasanjo na nuna tsantsar adawarsa, hakan ba zai taba bashi nasara wajen hana shugaban kasa Muhammadu Buhari zarcewa a zaben 2019 ba.

Da ya ke jawabi da jaridar Daily Independent, Momo, daya daga cikin shuwagabannin jam'iyyar APC a Nigeria, ya ce musamman ma yan Arewa ba za su saurari Obasanjo ba ko da kuwa ya bukace su da su zabi wata jam'iyyar banda APC.

A tuna abubuwan da suka faru a baya, Momoh ya ce Obasanjo ya yi kokarin kitsa tuggun murdiyar zaben gwamnan jihar Kano a 2003, don taimakawa Kwankwaso, amma Buhari ya yi masa kafar Angulu wanda ya ke goyon bayan Mallam Ibrahim Shekarau.

Prince Momoh: Tsananin kiyayyar Obasanjo ba za ta hana Buhari yin tazarce a 2019 ba

Prince Momoh: Tsananin kiyayyar Obasanjo ba za ta hana Buhari yin tazarce a 2019 ba
Source: Twitter

Ya ce a lokacin Obasanjo ne ke shugabantar kasar, inda aka samu kuri'u miliyan 12, a lokacin Obasanjo ya yi kokarin tabbatar da Kwankwaso a matsayin gwamna, amma Buhari ya goyi bayan Shekarai. Daga karshe dai dole Obasanjo ya hakura aka tabbatar da Shekarau a matsayin gwamnan Kano a 2003.

KARANTA WANNAN: Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna

"Don haka, Obasanjo ya san ba zai iya dakatar da Buhari ba. Mutum daya ne kadai zai iya kada Buhari shi ne wanda ke da kuri'a a hannunsa. Shin wace kuri'a ce Obasanjo zai samu a Arewa ko Kudu maso Yamma da zai bashi nasarar kayar da Buhari? Shin yana ma da kuri'a a mahaifar tasa ta Egbaland da zai kada Buhari kuwa? "a cewar Momoh.

Prince Momoh ya bayyana cewa suna nan suna jiran yadda ADC za ta samu nasara tunda dai ita ce jam'iyyar da Obasanjo ya ke goyon baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel