Shugaba Buhari ya baiwa iyalan wani Ministansa daya rasu kyautar katafaren gida

Shugaba Buhari ya baiwa iyalan wani Ministansa daya rasu kyautar katafaren gida

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cika alkawarin data daukan ma iyalan tsohon minista James Ocholli daya rasu a sanadiyyar hadarin mota daya rutsa da shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kafin rasuwansa, Ocholli ne karamin ministan kwadago, kuma ya rasu ne watan Maris na shekarar 2016 akan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga babban birnin tarayya Abuja a lokacin da tayar motarsa ta fashe.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da karamin yaron shugaban jam’iyyar APC daga makaranta

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya mika wannan kyautan katafaren gida ga iyalan tsohon Ministan kamar yadda Buhari ya dauki alkawari, inda yace sun yi haka ne don cika wannan muhimmin alkawari.

A yayin mika makullan gidan, Boss Mustapha wanda ya samu wakilcin babban sakataren ayyuka, Olusegun Adekunle yace wannan gidan na daga cikin alkawurra guda uku da gwamnati ta daukan ma iyalan mamacin a yayin bikin binneshi.

Daukan nauyin karatun yayansa, baiwa yayansa da suka kammala karatu aikin yi da kuma kyautar gida a babban birnin tarayya Abuja, sune alkawurra guda uku da gwamnatin shugaba Buhari ta daukan ma iyalan Ocholli.

Boss ya cigaba da cewa: “Shugaban kasa ya dauki wannan alkawari ne duba da jajircewa da kuma sadaukarwa da mamacin yake nunawa a bakin aiki a lokacin yana raye. Gida ne mai dakuna hudu a rukunin gidaje na Flower dake kan titin Apo Abuja.”

Dayake amsan takardu da makullan gidan a ofishin sakataren gwamnatin, a madadin iyalan Ocholli, babban dansa Aaron ya yaba ma gwamnati data cika alkawarin data dauka.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel