Buhari ba ya da hangen nesa da zai iya ciyar da Najeriya gaba - Saraki

Buhari ba ya da hangen nesa da zai iya ciyar da Najeriya gaba - Saraki

A yayin da adawa da hamayya ke ci gaba da tafarfasa a zukatan 'yan siyasar kasar nan, mun samu cewa shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, ya yi kaca-kaca da shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da fede ma sa Biri har Wutsiya.

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa, ko kadan shugaba Buhari ba ya da wata cancanta ta fuskar hangen nesa da juriya da za su tabbatar da ci gaban kasar nan ta Najeriya.

Kamar yadda shafiin jaridar The Punch ya ruwaito, Saraki ya bayyana cewa ba bu wani hobbasa da kasar nan za ta yi ta fuskar ci gaba muddin shugaba Buhari da jam'iyyarsa ta APC za su ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki ta Najeriya.

Buhari ba ya da hangen nesa da zai iya ciyar da Najeriya gaba - Saraki

Buhari ba ya da hangen nesa da zai iya ciyar da Najeriya gaba - Saraki

Saraki ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, inda ya jagoranci kungiyar yakin neman zabensa zuwa fadar gwamnatin jihar dake babban birni na Yenagoa.

Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya kirayi al'ummar Najeriya akan su daura damarar sauya gwamnatin jam'iyyar APC, da ba bu abinda ta tsinana a kasar nan face rabuwar kan al'ummar ta.

KARANTA KUMA: Gwamnonin APC 10 dake neman tazarce a zaben 2019

Tamkar kowane dan siyasa, Saraki ya bayyana cewa ba bu wani shugaba mafi cancatar jagoranci a kasar nan da ya wuce mutum mai jini a jiki kamar sa, inda ya ce a halin yanzu kasar nan na bukatar jagora da zai hada kan al'ummar ta wuri guda.

Saraki ya kara da cewa, matukar al'ummar Najeriya su na muradin sauya fasalin kasar nan, to kuwa ba bu shakka su sha kuruminsu domin shine shugaba mafi cancantar tabbatar da hakan muddin su kada ma sa kuri'un su a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel