An sake kwatawa: Ambaliya ya lalata gidaje da dama, ya halaka mutane 11 a Jigawa

An sake kwatawa: Ambaliya ya lalata gidaje da dama, ya halaka mutane 11 a Jigawa

Akalla mutane goma sha daya ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wani ambaliyan ruwa mai karfi da aka sake samu a kananan hukumomin Jahun da Auyo dake cikin jahar Jigawa, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan ayyuka na jahar, Aminu Mahmud ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labaru a yayin wata ganawa da yayi dasu a ranar Alhamis a garin Dutse.

KU KARANTA: Yan bindiga sun yi garkuwa da karamin yaron shugaban jam’iyyar APC daga makaranta

Kwamishina Mahmaud yace tuni gwamnatin jahar ta kwashe mutanen da ambaliyar ta shafa zuwa sansanin yan gudun hijira da nufin su cigaba da zama a wajen har zuwa lokacin da ruwan zai tsagaita.

Jahar Jigawa dai na daga cikin jihohin dake fama da matsalar ambaliya a damunar bana, kuma tana daga cikin jihohin da hukumar bada agajin gaggawa, NEMA, ta yi gargadin zasu fuskanci matsanancin ambaliya sakamakon mamakon ruwan sama da za’a sha a wasu yankunan.

A cewar NEMA, ruwan dake tafkin Benuwe da na Neja zai karu sosai har ma ya hauhawa, daga nan ne zai fita zuwa manyan hanyoyin ruwa inda zai iya janyo ambaliya a wurare da dama, daga cikin jihohin da abin yafi shafa a cewar NEMA har da Neja, Edo, Anambra, da Bayelsa.

A sakamakon wannan ambaliya daya shafi jihohin da aka Ambato, an samu mace macen rayuka guda saba’in, gidaje da dama sun nutse a cikin ruwa, yayin da dubunnan mutane suka rasa matsuguninsu.

Ko a yan kwanakin nan sai da ruwa ya halaka mutane shida a kauyen Dabi dake cikin karamar hukumar Ringim, sai dai duk wannan jarrabin, hukumar kula da albarkatun ruwa ta Najeriya, NIHSA ta yi gargadin akwai sauran aiki a gaba sakamakon cigaba da hauhawar ruwa a tafkunan Najeriya.

A nata bangaren, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shirya kaddamar da dokar ta baci akan matsalolin ambaliyan ruwan da ake fuskanta, matukar hasashen da ake yin a karuwar ambaliyan ya tabbata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel