2019: Atiku ya fara shiryawa takara a karkashin Jam’iyyar PDP gadan-gadan

2019: Atiku ya fara shiryawa takara a karkashin Jam’iyyar PDP gadan-gadan

Mun samu labari cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya nada kwamitin da su taya sa yakin neman zaben Shugaban kasa a shirin da yake cigaba da yi na samun takara a zaben 2019.

2019: Atiku ya fara shiryawa takara a karkashin Jam’iyyar PDP gadan-gadan

Atiku ya sa su Iwuanyanwu cikin kwamitin neman tikitin PDP
Source: Depositphotos

Atiku Abubakar ya sa Emmanuel Iwuanyanwu da kuma wasu manyan mutane 58 a cikin kwamitin yakin neman takarar da yake yi a PDP. Wannan kwamiti za tayi kokarin taimakawa Atiku wajen samun tikitin Jam’iyyar adawar.

Darektan yakin neman zaben Atiku watau Gbenga Daniel ya tabbatar da wannan nadi da aka yi inda yace an zabi mutane daga kowane bangare na kasar nan da za su taimaka wajen ganin Atiku ya samu tutar PDP a zaben 2019.

Tsohon Gwamna Gbenga Daniel ya bayyana cewa za a fadada kwamitin da zarar Atiku ya samu nasara a zaben fitar da gwanin da za ayi kwanan nan. Hakan zai bada dama Atiku ya kara da Shugaba Buhari da kyau a 2019.

KU KARANTA: APC ta tsaida ranar da za a fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa

Emmanuel Iwuanyanwu yayi jawabi a bakacin sauran ‘yan kwamitin da aka nada a jiya Alhamis inda ya ji dadin yadda aka zabo su da su yi wannan aiki yana mai sa rai za su samu nasara a zaben fitar da gwani da kuma babban zabe.

Atiku zai kara ne da irin su Rabiu Kwankwaso, Ahmad Makarfi, Bukola Saraki, Aminu Tambuwal, Attahiru Bafarawa, Sule Lamido, Ibrahim Dankwambo, Tanimu Turaki da ma su David Mark da Jonah Jang da sauran su a Jam'iyyar PDP.

Jiya kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya soki Buhari inda yace ana kokarin murde zaben Gwamna a Osun bayan ‘Yan Sanda sun taso ‘Dan takarar PDP a gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel