Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

- Wani Fasto mai kambun baka, Mike Agboola ya yi hasashen wanda zai kashe zaben gwamna da za'ayi ranar Asabar a jihar Osun

- A yayin da ya ke wa'azi ga mabiyansa a ranar 2 ga watan Satumba a cocinsa, Agboola ya ce zaben tana tattare da abubuwa masu daure kai

- Ya kuma ce Sanata Ishola Iyiola Omisore na jam'iyyar Socila Democratic Party shine zai lashe zaben

Wani Fasto kuma shugaban Jehovah Power Tabernacle, Prophet Mike Agboola ya yi hasashen dan takarar da zai lashe zaben gwamna da za ayi ranar 22 ga watan Satumban 2018 a jihar Osun.

A yayin da ya ke wa'azi ga mabiyansa a ranar 2 ga watan Satumba, Agboola ya bayyana wanda zai lashe zaben da kuma wanda zai biye masa har ma da na uku inda ya ce Allah ne ya yi masa wahayi.

Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun

Wani mai kambun baka ya yi hasashen matsayin da APC da PDP za su tsinci kansu a zaben Osun
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Oyo tayi karin haske kan rufe gonar Obasanjo

Faston ya yi alfaharin cewa hasashen da ya yi game da zaben gwamna na jihar Ekiti ta zama gaskiya saboda Allah ne ke bayyana masa wadanda za suyi nasarar.

Kafin ya bayyana sunayen 'yan takarar da zai lashe zaben, Prophet Agboola ya ce wannan karon zaben zai bawa mutane mamaki domin ba abinda aka saba gani zai faru ba. Ya ce dan takarar PDP Sanata Ademola Adeleke shine zai zo na uku.

Ya ce babban jami'in tsaron gwamna mai barin gado kuma dan takarar APC, Gboyega Oyetola shine zai zo na biyu kana wanda zai lashe zaben shine dan takarar jam'iyyar SDP, Sanata Ishola Iyiola Omisore.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel