Gwamnatin tarayya ta samu amincewar kotu domin kama wani Sanatan PDP

Gwamnatin tarayya ta samu amincewar kotu domin kama wani Sanatan PDP

Kwamitin da shugaba Buhari ya kafa domin kwato kadarar gwamnati da wasu tsiraru suka mallaka ba bisa ka'ida ba ya samu sahalewar kotu domin kama Sanata Peter Nwaoboshi bisa tuhumar sa da karkatar da dukiyar jama'a da cin hanci.

Wata kotun majistare dake Wuse II ne karkashin jagorancin mai shari'a Akanni Olaide ta bawa kwamitin takardar izinin kama Sanata Nwaoboshi a ranar 18 ga wata.

A yau, Alhamis, ne kakakin kwamitin, Lucie-Ann Laha, ta gabatar da kwafin izinin kama Sanata Nwaoboshi ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Abuja.

Gwamnatin tarayya ta samu amincewar kotu domin kama wani Sanatan PDP

Gwamnatin tarayya ta samu amincewar kotu domin kama wani Sanatan PDP
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

Kwamitin na zargin Sanata Nwaoboshi da mallakar kadarori da almubazzaranci da dukiyar jama'a da yawansu ya kai biliyan N3.48bn.

Ana zargin Sanatan na jiha Delta da mallakar gidaje, kamfanoni, rukunin gidajen haya na biliyoyin Naira a Asaba, babban birnin jihar Delta.

A cewar kwamitin, Nwaoboshi ya yi amfani da haramtattun kudaden da ya karkatar wajen wani gida a unguwar Apapa dake Legas da kuma wani gidan a Landan, babban birnin kasar Ingila.

Nwaoboshi ya aikata wadannan laifuka ne lokacin da yake rike da mukamin kwamishina a jihar Delta.

Yayin da NAN suka tuntubi Nwaoboshi sai wani mutum ya daga kiran tare da sanar da su cewar kwamitin bai taba gayyatar Sanatan ba.

Kazalika, hukumar EFCC na tuhumar Sanata Nwaoboshi da laifukan cin hanci na kudi, miliyan N805, a wata kotu dake Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel