Kishin-kishin: Wani gwamna a Arewa yayi karin haske game da maganar komawar sa PDP

Kishin-kishin: Wani gwamna a Arewa yayi karin haske game da maganar komawar sa PDP

- Gwamna Lalong yayi karin haske game da maganar ficewar sa jam'iyyar APC

- Yace labarin kanzon kurege ne hakan

- Yace shi bai taba ma tunanin fita daga APC ba

Mista Yakubu Dati da ke zaman kwamishin yada labarai da harkar sadarwar jihar Filato dake a shiyyar Arewa ta tsakiya ya karyata batun da ke yawo na yiwuwar ficewar gwamnan jihar, Simon Bako Lalong daga APC.

Kishin-kishin: Wani gwamna a Arewa yayi karin haske game da maganar komawar sa PDP

Kishin-kishin: Wani gwamna a Arewa yayi karin haske game da maganar komawar sa PDP
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Zan gyara Najeriya cikin shekaru 2 kacal - Mark

A cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun sa da ya fitar, Mista Yakubu ya ce ba'a taba ma samun rana daya ko lokacin da gwamnan ya yi sha'awar fita jam'iyyar sa ta APC ba balle kuma ma ace har yana son komawa PDP.

Legit.ng ta samu daga kwamishinan cewa wannan karin hasken daga gare shi ya zama dole ne musamman ganin yadda labarin kanzon kuregen ficewar ta sa ke ta yawo a gari da bakunan mutane.

A wani labarin kuma, An samu sabanin fahimta a tsakanin mutane biyu daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a shekarar 2019 a babbar jam'iyyar adawa ta PDP da kuma daya daga cikin jiga-jigan ta na kasa kuma gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike.

'Yan takarar dai da suka samu sabanin fahimtar da Gwamna Wike sun hada da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo da kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a lokacin mulkin shugaba Jonathan, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel