An hurowa sabon shugaban DSS wuta ya saki Zakzaky da Dasuki

An hurowa sabon shugaban DSS wuta ya saki Zakzaky da Dasuki

- An hurowa sabon shugaban DSS wuta ya saki Zakzaky da Dasuki

- Kungiyar Platform for Justice, Transparency and Good Governance ce ta bukaci hakan

- Kotu dai ta bayar da belin su amma ba'a sake su ba har yanzu

Wata kungiya ma zaman kanta da ba ta gwamnati ba mai rajin tabbatar da mulkin adalci, kamanta gaskiya da kuma kare hakkin bil'adama mai suna Platform for Justice, Transparency and Good Governance, a turance ta bukaci sabon shugaban hukumar DSS, Yusuf Bichi da ya sake duba lamarin wadanda hukumar ke cigaba da tsarewa.

An hurowa sabon shugaban DSS wuta ya saki Zakzaky da Dasuki

An hurowa sabon shugaban DSS wuta ya saki Zakzaky da Dasuki

KU KARANTA: Yan sanda sun garkame sakatariyar jam'iyyar APC

Shugaban kungiyar mai suna Nazir Galadanci shine ya bayyana wannan bukatar ta kungiyar ga manema labarai lokacin da ya zanta da su a ofishin su dake a garin Abuja.

Legit.ng ta samu cewa Nazir ya ce ya kamata hukumar ta sake duba ga wadanda take cigaba da tsarewa duk kuwa da umurnin kotu na cewa a sake su kamar irin su Ibrahim Zakzaky da Sambo Dasuki.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin masu neman tikitin takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya zabe mai zuwa na shekarar 2019 a karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yiwa gwamnatin shugaba Buhari wankin babban bargo.

Attahiru Bafarawa, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto ne ya yi ikirarin cewa ba abunda gwamnatin ta shugaba Buhari ta jawowa 'yan Najeriya cikin shekaru ukun su a kan mulki sai bala'I da masifa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel