Mutum 10 sun mutu sadda fada ya kaure a wajen taron jiga-jigan jam'iyyar APC

Mutum 10 sun mutu sadda fada ya kaure a wajen taron jiga-jigan jam'iyyar APC

- Mutum 10 sun mutu a wajen taron jiga-jigan jam'iyyar APC

- Lamarin ya auku a jihar Abia

- Wasu da yawa kuma sun jikkata

Akalla mutane 10 ne aka tabbatar da mutuwar su lokacin da wani kazamin fada ya kaure a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta jihar Abia dake a shiyya kudu maso gabashin Najeriya.

Mutum 10 sun mutu sadda fada ya kaure a wajen taron jiga-jigan jam'iyyar APC

Mutum 10 sun mutu sadda fada ya kaure a wajen taron jiga-jigan jam'iyyar APC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: 2019: Yawan mutanen da ke neman tikitin takarar gwamna a PDP

Kamar dai yadda muka samu an dai gabza fadan ne a kauyen Okpuala Aro dake a karamar hukumar Osisioma Ngwa ta jihar ta Abia.

Legit.ng ta samu daga majiyar mu cewa wasu matasa ne dai suka je har hedikwatar jam'iyyar ta APC dake a kuayen Okpuala Aro suka fara dukan zababbun shugabannin jam'iyyar kafin daga bisani fadan ya kacame.

Haka zalika mun samu cewa matasan dai sun tafka wannan aika-aikar ne jim kadan bayan da dan takarar kujerar Sanata na shiyyar jihar ta tsakiya a jam'iyyar ya bar hedikwatar a cigaba da rangadin neman jama'a da yake yi.

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ne ya nada sabon madugun yakin neman zaben sa na tazarce a shekarar 2019 mai zuwa ganin cewa lokaci na ta kara karatowa.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da mai taimakawa shugaban kasar akan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel