Wata sabuwa: An samu sabanin fahimta tsakanin 'yan takarar shugaban kasa 2 da Wike

Wata sabuwa: An samu sabanin fahimta tsakanin 'yan takarar shugaban kasa 2 da Wike

- An samu sabanin fahimta tsakanin 'yan takarar shugaban kasa 2 da Wike

- Shi yace APC na goyon bayan wani dan takarar PDP

- Su kuma sunce basu yadda ba

An samu sabanin fahimta a tsakanin mutane biyu daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a shekarar 2019 a babbar jam'iyyar adawa ta PDP da kuma daya daga cikin jiga-jigan ta na kasa kuma gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike.

Wata sabuwa: An samu sabanin fahimta tsakanin 'yan takarar shugaban kasa 2 da Wike

Wata sabuwa: An samu sabanin fahimta tsakanin 'yan takarar shugaban kasa 2 da Wike
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan sanda sun maka wani dan takarar gwamna a PDP kotu

'Yan takarar dai da suka samu sabanin fahimtar da Gwamna Wike sun hada da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo da kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a lokacin mulkin shugaba Jonathan, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki.

Legit.ng ta samu cewa batun da ya jawo rabuwar kan dai shine na ikirarin cewar akwai wasu 'yan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP da APC take goyon baya da shi gwamnan yayi a farkon satin nan.

Sai dai dukkan 'yan takarkarin sun bayyana cewa tare da ganin girman sa da suke yi, amma suna ganin ba kanshin gaskiya a cikin zancen domin kuwa dukkanin su kishin kasa ne yasa suke neman takarar.

A wani labarin kuma, Mista Yakubu Dati da ke zaman kwamishin yada labarai da harkar sadarwar jihar Filato dake a shiyyar Arewa ta tsakiya ya karyata batun da ke yawo na yiwuwar ficewar gwamnan jihar, Simon Bako Lalong daga APC.

A cikin wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun sa da ya fitar, Mista Yakubu ya ce ba'a taba ma samun rana daya ko lokacin da gwamnan ya yi sha'awar fita jam'iyyar sa ta APC ba balle kuma ma ace har yana son komawa PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel