2019: Buhari ya kafa kwamitin yakin neman zabensa

2019: Buhari ya kafa kwamitin yakin neman zabensa

- Shugaban kasa muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin da zai yi masa yakin neman zabe a shekarar 2019 karkashin jagorancin Chibuike Rotimi Amaechi

- Amaechi ya rike mukamin shugaban majalisar Ribas kafin daga bisani ya zama gwamnan jihar. Yanzu haka shine ministan sufuri na kasa

- Ko a shekarar 2014-2015, Amaechi ne ya jagoranci kwamitin yakin neman zaben Buhari har ya kai ga jam’iyyar APC ta samu nasara a zaben shekarar 2015

A wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaba Buhari ya fitar, ya bayyana cewar bisa amincewar Amaechi zai zabi ragowar mambobin kwamitin da zasu yi aiki tare bayan sahalewar shugaban kasa.

A wani rahoton na Legit.ng, kun ji cewar a yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, shugabancin jam’iyyar APC na kasa ya amince da bukatar shugabancin jam’iyyar na jihohi tare da basu dammar amfani da hanyar da suke so domin gudanar da zabukan fitar da ‘yan takara, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

2019: Buhari ya kafa kwamitin yakin neman zabensa

Buhari da Amaechi
Source: Depositphotos

Legit.ng ta samu rahoton cewar APC ta yanke wannan shawara ne bayan ganawar fiye da sa’o’i uku da aka yi jiya, Laraba, tsakanin shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da gwamnonin APC 22 a gidan gwamnatin jihar Imo dake unguwar Asokoro a Abuja.

DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya amince da korar wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya 6

Oshiomhole ya bayyana cewar yanzu jihohin zasu ci gashin kansu a kan batun hanyar da zasu yi amfani da ita domin fitar da ‘yan takara bisa sharadin cewar zasu nemi amincewar masu ruwa da tsaki na APC a jihohinsu.

Gwamnonin APC ne suka kafe kan cewar jam’iyyar ba zata yi amfani da zaben ‘yar tinke ba bayan uwar jam’iyyar ta amince da hakan yayin taron gudanawar na kasa a kwanakin baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel