Ministan Buhari ya bayar da umarnin korar wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya 6

Ministan Buhari ya bayar da umarnin korar wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya 6

Ministan sharia na kasa, Abubakar Malami, ya amince da koarar wasu ma’aikatan hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) guda shida ta hanyar tilasta su yin ritaya tare da kakabawa wasu karin ma’aikatan hukumar biyu takunkumi bayan samun su da laifukan da suka saba da ka’idojin aikin hukumar.

Ministan ya amince da korar ma’aikatan ne bayan kwamitin bincike da hukumar NAPTIP ta kafa ya tabbatar da samun su da aikata laifuka da dama.

Batun korar ya matukar girgiza ragowar ma’aikatan hukumar, sai dai hukumar ta NAPTIP ta bayyana cewar hukuncin da ta yanke na daga cikin matakan tsaftace aiyukan hukumar da kuma cusa da’a, biyayya da girmama dokokin aiki a zukatan ma’aikatan hukumar.

Hukumar ta kara da cewa ta yi amfani da dokokin aikin gwamnati da na kwadago wajen yankewa ma’aikatan hukunci bayan samun su da laifuka daban-daban.

Ministan Buhari ya bayar da umarnin korar wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya 6

Abubakar Malami
Source: Depositphotos

A wata takardar sanarwa da hukumar ta raba ga ma’aikatan da abin ya shafa, hukumar NAPTIP ta zayyana laifukan ma’aikatan da suka hada da karbar cin hanci, bayar da muhimman bayana a kan aikin hukumar, hada baki da masu safarar mutane, karbar kudi domin taimakon masu laifi da hukumar ta tsare da kuma yiwa masu laifi hanyar tserewa bayan an kama su.

DUBA WANNAN: Sabon shugaban hukumar tsaro ta DSS ya ziyarci Buhari (Hotuna)

Ragowar laifukan sun hada da lalata da wadanda aka kubutar daga hannun masu safarar mutane, barin wurin aiki na fiye da shekara guda ba tare da izinin hukumar ba da sauran su.

Darekar hukumar NAPTIP, Julie Okah-Donli, ta shaidawa jaridar Daily Trust cewar duk da babu dadi a kori ma’aikaci, korar ma’aikatan ba kuskure bane idan aka kalli laifukan da suka aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel