Babban bankin CBN na duba hujjoji da Bankuna da MTN suka kawo kan tarar da yayi musu

Babban bankin CBN na duba hujjoji da Bankuna da MTN suka kawo kan tarar da yayi musu

- Muna kara duba shaida ta bankuna hudu

- Nagartar CCI na nan, babu mai bata ta

- Babban bankin na maraba da masu zuba hannayen jari

Babban bankin CBN na duba hujjoji da Bankuna da MTN suka kawo kan tarar da yayi musu

Babban bankin CBN na duba hujjoji da Bankuna da MTN suka kawo kan tarar da yayi musu
Source: Depositphotos

Babban bankin Najeriya na kara duba shaidun bankuna hudu da kamfanin sadarwa na MTN akan hukuncin da yayi musu.

Bankunan - Standard Chartered, Stanbic, Citi da Diamond babban bankin yaci tarar Naira biliyan 5.87 saboda karya dokar capital importation.

Babban bankin ya zargi bankunan mu'amala da wasu cinikayya na kasashen waje da basu da takardar CCI ingantacciya na kamfanin MTN. Bankunan da MTN sun Musa hakan.

DUBA WANNAN: Cututtuka 8 da suka fi kashe yan Najeriya

A yanzu dai bankunan da MTN sun samar da karin bayani, wanda a halin yanzu ake dubawa don samo maslaha.

Suna kuma tabbatar wa da masu zuba hannayen jari cewa Nagartar CCI bazata taba samun nakasa ba kuma suna maraba da masu zuba hannayen jari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel