Yaki da rashawa: Alkalin Kotu ya watsa ma wani tsohon gwamna kasa a ido kan badakalar N7.6

Yaki da rashawa: Alkalin Kotu ya watsa ma wani tsohon gwamna kasa a ido kan badakalar N7.6

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Legas ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan jahar Abia, na hannun daman Buhari, kuma jigo a cikin jam’iyyar APC, Orji Uzo Kalu, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jigon na APC ya bukaci Kotu ta yi fatali da karar da hukumar yaki da zamba da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta shigar dashi kan zarginsa da handame makudan kudi naira biliyan 7.6 mallakan gwamnatin jahar Abia a zamanin dayake gwamna.

KU KARANTA: Zaben shugaban hukumar kwallon kafa: Yadda Amaju ya sake zarcewa a Katsina

Kamfanin Kalu, Slok Nigeria Limited da wani Ude Udeogu ne suka bukaci kotun da ta dakata da shari’ar da ake yi musu sakamakon wasu kararraki da suka daukaka zuwa kotunan gaba, duk da cewa kuwa sun samu sammacin daga Kotun akan cewa za’a cigaba da zama a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Yaki da rashawa: Alkalin Kotu ya watsa ma wani tsohon gwamna kasa a ido kan badakar N7.6

Uzo Kalu
Source: Depositphotos

Lauyan Kalu, K.C Nwafor ne ya mike a gaban Kotu, inda ya shaida ma Alkalin Kotun cewa ya daukaka kata gaban kotun daukaka kara bisa watsi da kotun ta yi da bukatar wanda yake karewa da ya shaida mata cewa shi ba shi da laifi a cikin karar da ake yi masa.

Don haka Nwafor yace yana kalabalantar hurumin alkalin babbar kotun, Mai shari’a Muhammed Idris na cigaba da sauraron karar, tun da dai an dauke Alkalin daga babbar kotun zuwa kotun daukaka kara.

Sai dai a wani mataki mai kama da ranin hankali, a baya an samu wani lauyan Kalu, Farfesa Awa Kalu daya nemi shugaban kotun daukaka kara, Mai shari Zainab Bulkachuwa data baiwa Alkalin dake sauraron karar tasu Muhammed Idris daman cigaba da shariar duk da cewa an kara masa girma.

Haka kuwa aka yi, sai Bulkachuwa ta baiwa Alkali Idris umarnin cigaba da sauraron karar, amma fa da sharadin daga karshen watan Satumba zai saki karar ya wuce gaba don kama sabon aikinsa a kotun daukaka kara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel