Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

- Shugaban sojin Kasa, Laftanant Janar Tukur Buratai ya bayar da umurnin kama dukkan wanda aka samu da bindiga a Filato

- Buratai ya bayar da wannan umurnin ne a ziyarar da ya kai karamar hukumar Riyom da ke jihar Filato

- Ya kuma umurci dakarun sojin su binciko bata garin da ke kafa shinge a tituna suna kashe mutane

Shugaban hafsoshin Sojin kasa na Najeriya, Laftanant Tukur Yusuf Buratai, ya umurci dakarun sojin Operation Safe Haven da ke aikin samar da zaman lafiya a wasu jihohin Arewa da ke karamar hukumar Riyom na jihar Filato su kama duk wanda aka samu da bindiga.

Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

Ba sani ba sabo: Buratai ya bayar da umarnin kama duk wanda aka samu da bindiga a jihar da aka kashe wani soja

A yayin da ya ke yiwa sojojin jawabi wajen atisayen tsaro na Unit 6, Buratai ya gargadi sojojin su dena yin sakwa-sakwa da batun tsaro a jihar.

DUBA WANNAN: Zaben fitar da gwani: Oshiomhole da gwamnonin APC sun saka labule

Shugaban sojin ya kuma ce hukumar ba za ta amince da kafa shinge da wasu bata gari keyi a kan tituna ba, inda ya bukaci sojojin su dauki matakan binciko wadanda ke aikata wannan laifukan a garin.

Kazalika, Legit.ng ta ruwaito cewa wasu dakarun soji biyu da ke bataliyar 192 sun rasu sakamakon harba bindiga da wani sojin yayi cikin kuskure yayin da sojojin ke wani atsaye. Lamarin ya faru ne a jiya Laraba 19 ga watan Satumban 2018.

Kamar yadda Hukumar Sojin ta bayyana a shafinta na Twitter, Shugaban Hafsin Sojin Najeriya, Laftanant Janar Tukur Buratai ya umurci a kafa kwamiti da za ta gudanar da bincike kan afkuwar lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel