Dalilin da yasa na dakile tazarce na a matsayin gwamna - Tambuwal

Dalilin da yasa na dakile tazarce na a matsayin gwamna - Tambuwal

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa dalilin da yasa ya dakile tazarcensa a matsayin gwamna karkashin APC ya kasance saboda jajircewars nason hadin kai da cigaban Najeriya.

Ya bayyana hakan a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a lokain kamfen dinsa inda ya yi alkawarin samar da shugabani mai ike da nagarta da zai hada kan kasar idan har aka zabe si a matsayinshugaban kasa.

Dalilin da yasa na dakile tazarce na a matsayin gwamna - Tambuwal

Dalilin da yasa na dakile tazarce na a matsayin gwamna - Tambuwal
Source: Depositphotos

Tambuwal wanda ya kasance gwamnan jihar Sokoto ya fadamataron magoya baya da diligit na PDP a sakatariyar jam’iyyar cewa akwai bukatar ayi gaggawan zabar dan takara mai karfi da zai iya tsige gwamnatin APC wacce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta.

A cewarsa gwamnatin APC ta gazawa yan Najeriya matuka.

KU KARANTA KUMA: Hukumar Hisbah a Kano ta kama kwalaban giya miliyan 12

A aya Legit.ng ta rahot cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana karara tare da bayar da tabbacin cewa ba zai nemi takarar kujerar mataimakin shugaban kasar nan ta Najeriya ba a zaben 2019 sabanin yadda ake faman yadawa a lunguna da sako na kasar nan.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, jiharsa ta Ribas ita ya sanya a gaba duk da cewar wasu daga cikin manema takarar shugaban kasar nan su yi ma sa tayi tare da romon baka na kwadaitar da shi kan kasancewa abokin takararsu a yayin da suke shawagi da neman goyon bayansa.

Yayin ganawarsa da manema labarai a fadar gwamnatinsa dake birnin Fatakwal a ranar Alhamis din da ta gabata, Gwamna Wike ya bayyana cewa akwai manema takarar kujerar shugaban kasa da suka dauki alkawarin zai zamto mataimakin su amma ya hau kujerar na ki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel