Babbar magana: AGF Malami ya dau hayar kamfanonin Amurka don yada ayyukan Buhari a jaridun kasar

Babbar magana: AGF Malami ya dau hayar kamfanonin Amurka don yada ayyukan Buhari a jaridun kasar

- AGF Malami ya dau hayar kamfanonin Amurka don yada ayyukan Buhari a jaridun kasar ta Amurka

- A shekaru biyar da suka gabata, Malami ya yi amfani da makudan daloli wajen bata sunan gwamnatin Goodluck a kasar Amurka

- A wannan karon, Malami ya baiwa kamfanin Chennel Kafoo kwangilar gano kamfanonin Amurka da za su yi aikin

Ministan shari'a na kasa, Abubakar Malami, ya baiwa wasu kamfanonin Amurka guda biyu kwangilar yin rubuce rubuce da za su nuna kokarin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jaridun kasar Amurka.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wannan kuduri na Mr. Malami ya biyo bayan irin wannan aiki da ya gudanar shekaru 5 da suka gabata, inda ya rinka tona asirin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ta hanyar kashe makudan daloli don tattaunawa da manyan kafafen watsa labarai da ke Amurka.

A binciken da jaridar ta yi, ta gano cewa a farkon wannan shekarar ne Malami ya gana da wani kamfanin hulda da jama'a a nan Nigeria, Channel Koos, inda ya ba kamfanin kwangilar gano masa wasu kamfanoni a Amurka da zasu iya gudanar da rubuce rubuce na yada manufofi da ayyukan Buhari a manyan kafafen watsa labarai na kasar ta Amurka.

KARAMTA WANNAN: Duk da barazanar amfani da bindiga: Yan Shi'a sun gunar da zanga zanga a Abuja

Babbar magana: AGF Malami ya dau hayar kamfanonin Amurka don yada ayyukan Buhari a jaridun kasar

Babbar magana: AGF Malami ya dau hayar kamfanonin Amurka don yada ayyukan Buhari a jaridun kasar
Source: Depositphotos

Dukkanin rubuce rubucen da Malami ya ke, za su kasance ne suna bayyana ayyukan ci gaba da gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari ta kawo. Sai dai har zuwa yanzu ba a san ko nawa ne ministan ya biya kamfanin na Channel Koofas don gudanar da wannan aiki ba. Sai dai kamfanin ya kashe $8,000 don gano kamfanonin da ba su kwangilar.

Kamfanonin kasar ta Amurka da aka fara ba kwangilar; Mount Olive LLC, da ke da zama a Maryland, mallakin dan kasuwar Nigeria da Amurka, Olufemi Soneye, kamar dai yadda ya ke a cikin rahoton da aka aikawa sashen shari'a na Amurka don hadin guiwa da ofishin magatakarda na harkokin kasashen waje.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayar da wannan kwangilar ne don sanar da kasashen ketare irin ayyukan raya kasa da gwamnatin ta ke yi a Nigeria kamar yadda doka ta tanadar.

Sai dai har zuwa yanzu Mr. Malami bai amsa kiran waya ko barin ganawa da yan jarida ba, haka zalika bai mayar da sakwannin karta kwana da ake tura masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel