Daga karshe: Uwar jam’iyyar APC ta cimma matsaya a kan hanyar zaben fitar da ‘yan takara

Daga karshe: Uwar jam’iyyar APC ta cimma matsaya a kan hanyar zaben fitar da ‘yan takara

- Bayan doguwar muhawara a kan hanyar da za a yu amfabi da ita wajen fitar da ‘yan takara a APC, jam’iyyar ta cimma matsaya a kan batun

- Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewar yanzu kowacce jiha zata iya amfani da duk hanyar da ta ga dama

- Tun da fari jam’iyyar APC ta amince da amfabi da ‘yar tinke bayan taron masu ruwa da tsaki da tayi kwanakin baya

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, shugabancin jam’iyyar APC na kasa ya amince da bukatar shugabancin jam’iyyar na jihohi tare da basu dammar amfani da hanyar da suke so domin gudanar da zabukan fitar da ‘yan takara, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Legit.ng ta samu rahoton cewar APC ta yanke wannan shawara ne bayan ganawar fiye da sa’o’i uku da aka yi jiya, Laraba, tsakanin shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da gwamnonin APC 22 a gidan gwamnatin jihar Imo dake unguwar Asokoro a Abuja.

Daga karshe: Uwar jam’iyyar APC ta cimma matsaya a kan hanyar zaben fitar da ‘yan takara

Adams Oshiomhole
Source: Depositphotos

Oshiomhole ya bayyana cewar yanzu jihohin zasu ci gashin kansu a kan batun hanyar da zasu yi amfani da ita domin fitar da ‘yan takara bisa sharadin cewar zasu nemi amincewar masu ruwa da tsaki na APC a jihohinsu.

DUBA WANNAN: Amsar da IBB ya bani bayan na nemi ya goyi bayan takarar Buhari - Kalu

Gwamnonin APC ne suka kafe kan cewar jam’iyyar ba zata yi amfani da zaben ‘yar tinke ba bayan uwar jam’iyyar ta amince da hakan yayin taron gudanawar na kasa a kwanakin baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel