Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan jihar Legas a Fadar Villa

Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan jihar Legas a Fadar Villa

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga bayan labule da gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, a fadar shugaban kasa ta Villa dake unguwar Aso Rock a babban birni na tarayya.

Za ku ji cewa, ganawar ta sirrance ta fara gudana ne da misalin karfe 2.40 na ranar yau ta Alhamis a fadar shugaban kasa Buhari dake garin Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar ganawar tana gudana ne a sakamakon dambarwar siyasa da ta kunno kai tsakanin gwamna Ambode da kuma Ubangidansa, Asiwaju Bola Tinubu.

Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan jihar Legas a Fadar Villa

Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan jihar Legas a Fadar Villa
Source: Depositphotos

Legit.ng ta ruwaito, a halin yanzu gwamnan na fuskantar barazana ta rasa kujerarsa sakamakon wani manemin takarar kujerar da ya bullo karkashin jam'iyyar sa ta APC.

KARANTA KUMA: 2019: Ba zan nemi Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa ba - Nyesom Wike

Ambode bayan mallakar fam dinsa na bayyana kudirin sake neman takarar kujerar sa a karkashin jam'iyyar ta APC, ya lura cewa akwai wani dan takara na daban da tuni ya bayyana irin wannan ra'ayi kuma ba bu shakka zai iya kasancewa babban kalubale a gare sa.

Barazanar rasa kujerar siyasa ta Gwamna Ambode ta kunno kai yayin da dangartakar sa da Tinubu ke samun tangarda, inda rahotannin suka bayyana cewa akwai yiwuwar su raba gari inda kowanensu zai yi hannun riga da juna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel