Adeleke: Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya soki Gwamnatin Buhari

Adeleke: Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya soki Gwamnatin Buhari

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari a dalilin sammacin da Jami’an ‘Yan Sanda su ka aikawa ‘Da takarar PDP a zaben Osun.

Adeleke: Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku ya soki Gwamnatin Buhari

Atiku yayi tir da Buhari game da batun takardun shaidar WAEC din Adeleke
Source: Depositphotos

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa ‘Dan takaran PDP Atiku yayi tir da Shugaba Buhari ne bayan Jami’an tsaro sun hurowa Sanata Ademola Adeleke wuta ana tuhumar sa cewa bai da takardar shaida ta kamalla karatun Sakandare.

Adeleke ne ke neman Gwamnan Jihar Osun a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP kuma kwanan nan za ayi zaben. Atiku ya nuna takaicin sa na yadda ‘Yan Sanda ke neman Sanata Adeleke a daidai wannan marra da ake shirin yi zaben sabon Gwamna.

KU KARANTA: Gwamnan Osun ya fara biyan Ma’aikata albashi bayan shekara 3

Tsohon Mataimakin Shugaban na Najeriya yace da alamu cewa akwai karfa-karfa a lamarin Buhari ganin yadda aka kyale tsohuwar Ministar kudi Kemi Adeosun ta sulale daga Najeriya duk da tabbata cewa tayi aiki da takardun bogi.

Alhaji Atiku Abubakar ya kare ‘Dan takarar na PDP inda yace Hukumar WAEC ta tabbatar da cewa yayi jarrabawa alhali ma shi kan shi Shugaba Buhari bai iya nunawa Duniya takardar shaidar WAEC din sa ba sai dai ya dauki Lauyoyi su kare sa.

Tsohon ‘Dan takarar Shugaban kasar Atiku yayi tir da matakin da Buhari ya dauka inda yace akwai take-taken murde zaben Osun da za ayi. Tuni dai yanzu Shugaba Buhari ya nemi ‘Yan Sanda su dakatar da binciken Adeleke zuwa bayan zaben Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel