Zaben shugaban hukumar kwallon kafa: Yadda Amaju ya sake zarcewa a Katsina

Zaben shugaban hukumar kwallon kafa: Yadda Amaju ya sake zarcewa a Katsina

Anyi an kammala zaben shuwagabannin hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, wanda aka gudanar da shi a jahar Katsina, yankin Arewa maso yammacin Najeriya, inji rahoton da Legit.ng ta kalato.

Sai dai sakamakon zaben ya nuna shugaban hukumar mai ci, Amaju Pinnick ne ya sake lashe zaben, wanda hakan ke nufin zai zarce akan wannan kujera ta shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya a karo na biyu.

KU KARANTA: Abin kunya: Kotu ta kashe auren ma’aurata bayan Miji ya dirka da ma yan aikinsu ciki sau 2

Zaben shugaban hukumar kwallon kafa: Yadda Amaju ya sake zarcewa a Katsina
Amaju Pinnick
Asali: Twitter

Jadawalin sakamakon zaben ya nuna matsayin yan takarkarun gaba daya kamar haka;

Amaju Pinnick – kuri’u 34

Aminu Maigari – kuri’u 8

Taiwo Ogunjo – kuri’u 2

Chinedu Okoye – babu kuri’a ko daya

A gaba daya zaben an samu kuri arba’in da hudu ne daya hada da kuri’un hukumomin kwallon kafa na jihohi, kungiyar alkalan wasa, masu horas da kungiyoyin kwallon kafa, da kuma kungiyar yan wasan kwallon kafa ta Najeriya.

Shugaban kwamitin shirya zaben, Muhammed Katu ne ya sanar da sakamakon zaben, a gaban wakilan hukumar kwallon kafa ta Duniya, Luca Piazza da Solomon Mudege da ma sauran mahalarta wannan zabe.

A yanzu haka ana can ana cigaba da jefa kuri’u a zaben mukaman mataimakin shugaban hukumar na farko, da sauran mukaman hukumar kwallon kafa ta Najeriya a jahar Katsina.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel