Na fita daga APC, na dawo gida - Yakubu Dogara

Na fita daga APC, na dawo gida - Yakubu Dogara

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Yakubu Dogara ya alanta fitarsa daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a yau Laraba, 20 ga watan Satumba 2018.

Dogara ya isa Sakatariyar jam'iyya ne tare da dimbin magoya bayansa da suka nuna masa goyon baya.

Yace: "Na yanke shawaran dawowa,"

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Yakubu Dogara, ya dira hedwatan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP yanzu domin mayar da takardan takaransa karkashin jam’iyyar.

Wannan takarda da aka fi sani da Fom zai bashi daman sake takarar kujeran dan majalisan wakilai a jihar Bauchi.

Zuwa yanzu, kusan dukkan manyan da suka fita daga PDP a shekarar 2014 sun dawo yanzu bayan shekara hudu a jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Allah zai tona asirin wadanda su ka kashe Sheikh Ja’afar-Shekarau

A bangare guda Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Aliyu Oshiomole, ya fara shirye-shiryen tsige kakakin majalisar wakilar, Yakubu Dogara, daga kujerarsa.

Wata majiya ta bayyanawa jaridar Cable cewa Oshiomole ya fara tattaunawa da mambobin jam’iyyar, musamman yan majalisan wakilai kan yadda za’a cire Dogara.

Majiyar ta kara da cewa shugaban jam’iyyar ya dauki wannan mataki bayan rahoton sauya shekar Dogara zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel