Yan bindiga sun kai farmaki ga wani Banki, sun kashe mutane 3 a Ekiti

Yan bindiga sun kai farmaki ga wani Banki, sun kashe mutane 3 a Ekiti

A ranar Laraba, 19 ga watan Satumba ne wasu gungun yan fashi da makami suka kai farmaki wani bankin dake cikin garin Igede na karamar hukumar Irepodun na jihar Ekiti da misalin karfe biyar na yamma, inji rahoton jaridar The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin wannan hari da suka kai, yan fashin sun kwashe tsawon mintuna 20 suna artabu da Yansanda, bayan sun warwatsu a ciki da wajen bankin, inda suka kashe ma’aikatan bankin guda biyu da Maigadin bankin.

KU KARANTA: Abin kunya: Kotu ta kashe auren ma’aurata bayan Miji ya dirka da ma yan aikinsu ciki sau 2

Bugu da kari Yan fashin sun fasa na’urar bada kudi ta ATM dake harabar bankin saboda tsananin harsashen da suka zuba mata, sa’annan daga bisani suka ranta ana kare a lokacin da Yansanda suka biyo su, kamar yadda kaakakin Yansandan yankin ya tabbatar.

Yan bindiga sun kai farmaki ga wani Banki, sun kashe mutane 3 a Ekiti

Bankin
Source: Depositphotos

Kaakaki Caleb Ikechukwu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an yi musayar wuta na kin karawa tsakanin yan bindigan da jami’an Yansandan SARS, amma yace daga bisani Yansandan sun raka yan fashin har cikin wani daji dake bayan gari.

Kaakaki Caleb ya tabbatar da mutuwar maigadin bankin, wanda yace nan take ya mutu ba ko shurawa, amma yace jami’an bankin guda biyu sun mutu ne a Asibiti, sai dai yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen kama yan fashin sakamakon a yanzu haka Yansanda sun zagaye dajin.

“A yanzu haka mun aika da karin jami’a Yansanda bankin don baiwa ma’aikata da masu hurda da bankin kariya, haka nan mun tura da rundunar Yansanda ta musamman zuwa garin Igede kamar yadda muka aika yansandan farin kaya wurare daban daban na jahar Ekiti.” Inji shi.

wannan harin banki da yan fashi da mamaki suke kaiwa ba shine na farko ba a yan kwanakin nan a yankin kudu masu yammacin kasarnan, inda ko a kwanakin baya ma sai da aka samu kwatankwacin wannan harin a Ado, Ikere, Ilasa, Ifaki, Otun, Okemesi da kuma garin Ilawe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel