Sake-saken aure: Mijina ya fiye gulma ga uwar karya, a raba mu - Mata ga Alkali

Sake-saken aure: Mijina ya fiye gulma ga uwar karya, a raba mu - Mata ga Alkali

Wata matar aure mai shekaru 43, Titilayo Akaba ta cukaci Kotun Customary da ke zaman ta a Top Garage ta raba aurenta da mijinta, Maselin Akada saboda ba za ta iya hakuri ta gulma da yawan karya da ya keyi ba.

Titilayo wadda ke sana'ar sayar da abinci a Baale Street, Torikah Badagry ta shaidawa kotu cewar ta taba kwana a bayan kanta saboda karyar da mijinta ya sharara.

Ta ce ta hadu da Maselin ne a shekarar 1997, su kayi aure ba tare da izinin iyayenta ba saboda ya girme ta da shekaru 30 kuma yanzu ta haifa masa yara uku duk da cewa bai ma biya sadakinta ba.

Sake-saken aure: Mijina ya fiye gulma ga uwar karya, a raba mu - Mata ga Alkali

Sake-saken aure: Mijina ya fiye gulma ga uwar karya, a raba mu - Mata ga Alkali
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Dan haya ya yiwa matar mai gida da dan ta duka

"Ya fiye son gulma da karya duk da yawan shekarunsa.

"Maselin ya rika birgima a kasa yana kuka ya ce na sace masa takardun karatunsa duk da cewa karya ce.

"Mijina ya kai ni kara caji Ofishin yan sanda na Area K da ke Morogbo ya yi kara ta cewa na aike 'yan daba su kashe shi.

"An mayar da shari'ar Ofihsin 'yan sanda na Badagary inda aka tsare ni na tsawon sa'o'i 24 kan abinda ban aikata ba," inji Titilayo.

Titilayo da roki kotun ta raba aurensu kuma ta bata ikon rike yaransu domin ba za ta iya cigaba da zama da makaryaci irin Maselin ba.

Shugaban kotun, Mr Sakirudeen Adekola ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Oktoba saboda wanda akayi karar bai hallarci kotun ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel