Yanzu-yanzu: Dogara ya dira hedkwatan PDP

Yanzu-yanzu: Dogara ya dira hedkwatan PDP

Kaakakin majalisar dattawa, Yakubu Dogara, ya dira hedwatan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP yanzu domin mayar da takardan takaransa karkashin jam’iyyar.

Wannan takarda da aka fi sani da Fom zai bashi daman sake takarar kujeran dan majalisan wakilai a jihar Bauchi.

Har yanzu dai kakakin majalisa bai bayyana karara cewa ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress, APC ba.

Yanzu-yanzu: Dogara ya dira hedkwatan PDP

Yanzu-yanzu: Dogara ya dira hedkwatan PDP
Source: Twitter

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Aliyu Oshiomole, ya fara shirye-shiryen tsige kakakin majalisar wakilar, Yakubu Dogara, daga kujerarsa.

Wata majiyata bayyanawa jaridar Cable cewa Oshiomole ya fara tattaunawa da mambobin jam’iyyar, musamman yan majalisan wakilai kan yadda za’a cire Dogara.

Majiyar ta kara da cewa shugaban jam’iyyar ya dauki wannan mataki bayan rahoton sauya shekar Dogara zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA: Kungiyar kwadago ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ko ta shiga yajin aiki

Har yanzu, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara bai bayyana fitarsa daga jam’iyyar APC ba duk da cewan yana musharaka cikin harkokinsu.

A watan Agusta, ya ki halartan taron masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC da akayi a Abuja.

A zaben majalisar dattawan mazabar jihar Bauchi ta kudu, jam’iyyar PDP ta lashe kuri’un karamar hukumar Yakubu Dogara, Bogoro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel