Hukumar Hisbah a Kano ta kama kwalaban giya miliyan 12

Hukumar Hisbah a Kano ta kama kwalaban giya miliyan 12

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama kwalaban giya sama da miliyan 12 daga hannun masu shigo da kaya a jihar a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

Shugaban hukumar, Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Kano a ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba.

Ya bayyana cewa hukumar tayi nasarar cafke barasar ne a ayyuka 800 da ta gudanar a kananan hukumomin 44 na jihar.

Hukumar Hisbah a Kano ta kama kwalaban giya miliyan 12

Hukumar Hisbah a Kano ta kama kwalaban giya miliyan 12
Source: UGC

Ya kuma bayyana cewa wannan aiki da suka gudanar a kokarinsu na ganin ba’a take doka ba, yasa sun yi nasarar kama motoci da dama da masu laifin ke amfani dasu wajen shigo da harmtattun kayayyaki cikin jihar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Rivers ta nemi ministan Buhari ya amayo N112bn na kadarorin da ya siyar

Shugaban hukumar ya kuma bayyana cewa zuwa yanzu sun lalata kwalabe miliyan 7.4 daga cikin kwalayen giya miliyan 12 da suka kama kamar yadda kotun dake shari’a kan lamarin tayi umurni.

Yace har yanzu ba’a kammala shari’an sauran kwalabe miliyan 4.7 da suka rage ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel