Mayakan Boko Haram sun tashi kauyuka guda 3, sun kashe mutane 7 a jahar Borno

Mayakan Boko Haram sun tashi kauyuka guda 3, sun kashe mutane 7 a jahar Borno

Mayakan Boko Haram sun sake kai wasu munanan hare hare a daren Laraba, 19 ga watan Satumba, inda suka babbaka wasu kauyuka guda uku a cikin karamar hukumar Konduga na jahar Borno, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mayakan sun kai hari ne a kauyukan Wanori, Kaleri, da Amarwa a cikin awanni biyu inda suka kona kauyukan kurmus, tare da kwashe kayayyakin abinci da suka samu a kauyukan.

KU KARANTA: Jerin wasu manyan ministoci guda 3 da suka ajiye aikinsu a gwamnatin Buhari

Nagartattun majiyoyi daga hukumomin tsaron Najeriya sun tabbatar da cewa yan bindigan sun isa kauyukan ne akan babura ta kan hanyatr Alau, “Kwatsam sai muka fara ganin hayaki na tashi daga kauyukan Dalori, Kaleri da Amarwa.

“Daga nan kuma sai karan harbe harbe muka fara ji daga yankin, sai dai dakaru Soji basu yi kasa a gwiwa ba nan da nan suka isa wajen a cikin jirgin yaki, nan fa aka dinga batakashi tsakanin Sojoji da yan ta’addan.” Inji su.

Wani mazaunin kauyen Amarwa, Goni Kachalla daya arce daga kauyen a lokacin da yan ta’addan suka dira, ya bayyana cewa sun fara harbin mai kan uwa da wabi ne a da suka isa kauyen suna ta kashe mutane babu gaira babu dalili. “A yanzu haka ban san inda iyalina suke ba” Inji shi.

Haka zalika Usma Grema wanda lamarin ya shafa ya tabbatar da cewa duk wani gida dake Kaleri yan bindigan sun kona shi, “Kowa yayi ta kansa ne kawai, don nima a yanzu haka na rasa duk wani abu da nake da shi.” Inji shi.

A nasa bangaren, shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Borno, Bello Danbatta ya bayyana cewa tuni hukumar ta aika da jami’anta zuwa kauyukan don kaima mutanen da harin ya shafa dauki, amma yace har yanzu bai kammala tattara adadin mutanen da suka mutu ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel