2019: Ba zan nemi Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa ba - Nyesom Wike

2019: Ba zan nemi Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa ba - Nyesom Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana karara tare da bayar da tabbacin cewa ba zai nemi takarar kujerar mataimakin shugaban kasar nan ta Najeriya ba a zaben 2019 sabanin yadda ake faman yadawa a lunguna da sako na kasar nan.

2019: Ba zan nemi Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa ba - Nyesom Wike

2019: Ba zan nemi Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa ba - Nyesom Wike
Source: Depositphotos

Kamar yadda gwamnan ya bayyana, jiharsa ta Ribas ita ya sanya a gaba duk da cewar wasu daga cikin manema takarar shugaban kasar nan su yi ma sa tayi tare da romon baka na kwadaitar da shi kan kasancewa abokin takararsu a yayin da suke shawagi da neman goyon bayansa.

Yayin ganawarsa da manema labarai a fadar gwamnatinsa dake birnin Fatakwal a ranar Alhamis din da ta gabata, Gwamna Wike ya bayyana cewa akwai manema takarar kujerar shugaban kasa da suka dauki alkawarin zai zamto mataimakin su amma ya hau kujerar na ki.

KARANTA KUMA: Buhari da Shugabanni 87 za su gabatar da jawabai a taron Majalisar 'Dinkin Duniya

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, ba ya da hannu cikin yanke shawarar gangamin jam'iyyar na kasa da za gudanar cikin jihar sa a ranakun 5 da 6 ga watan Oktoba, inda ya ce an fara tattauna batutuwan yanke shawarar hakan ba tare da masaniyarsa ba.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, sun yi tarayya da juna wajen kira ga al'ummar jihar Osun akan su kawo karshen shugabancin jam'iyyar APC yayin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a karshen wannan mako.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel