Gwamnatin Rivers ta nemi ministan Buhari ya amayo N112bn na kadarorin da ya siyar

Gwamnatin Rivers ta nemi ministan Buhari ya amayo N112bn na kadarorin da ya siyar

- Gwamnatin Jihar Rivers ta bayyana cewa Rotimi Amaechi na da tuhuma a kan sa game da zarginsa da ake yi da karkatar da kudaden tashar makamashin gas da ya sayar

- An zargi Ameachi da siyar da tashar gas din ga kamfani mai zaman kansa a lokacin da yake rike da mukamin gwamna

- An ce ya siyar da kadaran ne akan naira biliyan 112

Gwamnatin Jihar Rivers ta bayyana cewa Ministan dake kula da harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ya na da tuhuma a kan sa game da zarginsa da ake yi da karkatar da kudaden tashar makamashin gas da ya sayar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

An tattaro cewa Ameachi ya siyar da tashar gas din ga kamfani mai zaman kansa a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan jihar Rivers.

Gwamnatin Rivers ta nemi ministan Buhari ya amayo N112bn na kadarorin da ya siyar

Gwamnatin Rivers ta nemi ministan Buhari ya amayo N112bn na kadarorin da ya siyar
Source: Depositphotos

Kwamishinan labarai na jihar, Emma Okah, ya sanar da hakan a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba in da ya jadadda cewa Amaechi ya siyar da kadaran ne ga kamfanin mai na Sahara Energy, mallakar wani attajiri mai suna Tonye Cole.

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Matasa nake wakilta – Jerry Gana

An saida tashar ce a daidai lokacin da wa’adin Amaechi ke kusa da karewa a shekarar kafin zaben 2015.

Okah ya ce yayin da Amaechi ya siyar da tashar gas din har naira biliyan 112, ya yi amfani da kudin ne wajen gudanar da yakin neman zaben jam’iyyar All Procressives Congress mai mulki, wanda Amaechi din shi ne jagoran ta a jihar Rivers kuma shi ne Babban Daraktan yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a lokacin.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa wani tsohon jakadan Najeriya zuwa kasar Switzerland kuma daya daga cikin jiga-jigan da suka assasa jam'iyyar APC, Ambasada Yahaya Kwande, ya bayyana cewa har ila yau yana nan akan bakansa na ci gaba da goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Ambasada Kwande ya kuma bayyana cewa, ya halarci wani yawon shawagi da taron gangami na yakin neman zaben Atiku, manemin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar PDP domin tabbatar da biyayyarsa a gare shi da kuma goyon baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel