Mubaya’ar da aka yi wa Gwamna Abubakar ba za ta zauna ba – Pate

Mubaya’ar da aka yi wa Gwamna Abubakar ba za ta zauna ba – Pate

Mun samu labari cewa wasu ‘Yan takarar Gwamna karkashin Jam’iyyar APC mai mulki sun kai karar Gwamnan Jihar Bauchi Muhammad Abubakar da kuma APC ta Jihar a gaban Uwar Jam’iyya.

Mubaya’ar da aka yi wa Gwamna Abubakar ba za ta zauna ba – Pate

Dr. Muhammad Ali Pate yana da ja bayan an nemi Gwamna Abubakar ya zarce
Source: Depositphotos

Dr. Muhammad Ali Pate wanda yana cikin masu neman kujerar Gwamna a Bauchi yace ya rubuta wasika zuwa Hedikwatar Jam’iyyar APC inda su kayi kira ga Shugaban Jam’iyya da kuma manyan APC na kasa su duba lamarin Jihar.

‘Dan takarar na APC ya nemi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen rikicin da ya barke a Jam’iyyar a Bauchi. A makon jiya ne APC ta Jihar Bauchi ta dauki matakin cewa Gwamna Abubakar zai sake rike mata tuta a 2019.

Tsohon Ministan lafiyan ya nuna cewa ba su yi na’am da matakin da APC ta dauka ba har gobe a lokacin da ya bayyana a gaban gidan Talabijin Arise. Pate yace ba da bakin kowa aka yi wa Gwamnan mubaya’a ba don haka da sake.

KU KARANTA: Saraki ya maidawa Gwamnatin APC raddi bayan Buhari ya ziyarci Osun

Muhammad Ali Pate ya nemi manyan Jam’iyyar APC su duba abin da ya faru a Jihar Bauchi inda yace ba bi ka’idar Damukaradiyya ba. ‘Dan takarar yace shi da sauran masu neman Gwamna a Bauchi ba su yi amanna da matsayin APC ba.

Dr. Pate yace an kira su zuwa taron da APC ta daga hannun Gwamna Abubakar inda ya tura wakili yayin da sauran ‘Yan takarar su ka je da kan su. Sai dai yace an yi wa wakilin da ya tura dukan tsiya a gaban manya a cikin gidan Gwamnati.

Rigimar siyasa dai ta barke Jam’iyyar APC a wasu Jihohin inda ake rigima kan wadanda za su gaji Gwamnoni a wasu Jihohin. APC ta samu baraka ne a irin su Imo, Zamfara da Yobe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel