Zaben Shugaban kasa: Matasa nake wakilta – Jerry Gana

Zaben Shugaban kasa: Matasa nake wakilta – Jerry Gana

- Tsohon ministan bayanai, Farfesa Jerry Gana yace matasa ne suka bukaci ya yi takarar shugaban kasa

- Ya ce shi wakilin matasa ne kuma suna bayan shi a zaben 2019

- Jerry Gana dai na neman kujeran shugaban kasa ne a karkashin jam'iyyar SDP

Tsohon ministan bayanai, Farfesa Jerry Gana yace matasa ne suka bukaci ya shiga tseren takarar kujeran shugaban kasa a 2019.

Farfesa Gana wanda ke takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) yace: “Ni wakilin matasa ne, matasa suka bukaci da nemi takara kuma sunyi alkawarin mara mani baya sun kuma fara bani goyon bayansu.”

Zaben Shugaban kasa: Matasa nake wakilta – Jerry Gana

Zaben Shugaban kasa: Matasa nake wakilta – Jerry Gana
Source: Depositphotos

Yace a yanzu, kasar na bukatar cudanya na dattawa da matasa a gwamnati domin cigaba da tsirar kasar.

“Ba zaka iya karanta kwarewa a litattafai ba amma kana iya samun sa daga manya hakan ne dalilin da yasa akwai bukatar mu cudanya matasa da dattawa domin daukaka kasar saboda hakan zai zamo hadi mai tarin hikima," inji shi.

KU KARANTA KUMA: Zukata sun cika da tsoro a APC kan zaben fidda gwani

Yayi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta aiki na gaskiya da sunanta na mai zaman kanta sannan ta yi zaben 2019 cikin gaskiya da amana.

A cewarsa hakan zai sa yan takara gaba daya su amince da sakamakon zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel