Tambuwal ya caccaki Shugaban kasa Buhari bayan an dakatar da jirgin Najeriya

Tambuwal ya caccaki Shugaban kasa Buhari bayan an dakatar da jirgin Najeriya

Labari ya zo mana cewa ‘Dan takarar PDP a zaben Shugaban kasa a 2019 Aminu Waziru Tambuwal ya soki Gwamnatin nan ta Shugaban kasa Buhari sakamakon dakatar da shirin Nigerian Air da aka yi.

Tambuwal ya caccaki Shugaban kasa Buhari bayan an dakatar da jirgin Najeriya

Tambuwal yace da ka Gwamnatin Buhari ta ke aiki a Najeriya
Source: Depositphotos

Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya tofa albarkacin bakin sa a dalilin tsayar da yunkurin da Gwamnatin Najeriya ta soma na kafa kamfanin jiragen sama na kasar. Tambuwal yace an yi barnar kudin jama’a ne kurum a banza.

Aminu Tambuwal ya fito ta shafin sa na Tuwita ya bayyana cewa a dalilin rashin tsari, Gwamnatin Tarayya tayi watsi da sama da Naira Biliyan 1.5 daga dukiyar ‘Yan Najeriya wajen shirin na Nigerian Air wanda bai kai ko ina ba.

KU KARANTA: 2019: Wani Jigon APC yana tare da Atiku Abubakar

A jiya ne dai Ministan sufurin jiragen sama na kasar Hadi Sirika ya bayyana cewa Gwamntin Kasar ta dakatar da wannan yunkuri da yake yi bayan wani taron Majalisar zartawa na Tarayya watau FEC da aka yi a fadar Shugaban kasa.

Tambuwal yayi kira ga jama’a su mara masa baya ya samu mulkin kasar nan inda yace idan har ya zama Shugaban kasa ba za a rika barna da dukiyar jama’a ba. Tambuwal yace Gwamnatin sa za ta zama mai tsari ba irin ta Buhari ba.

A jiya kun ji cewa Gwamna Tambuwal ya kuma sha alwashin kawo karshen kashe-kashe a Najeriya idan aka zabe sa a 2019. ‘Dan takarar na PDP yace zai yi maganin rikicin da ake yi a irin su Benuwai, Taraba, Kaduna da Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel