Sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin atisaye

Sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin atisaye

Wasu jami’an sojoji Najeriya biyi sun rasa rayukansu sakamakon kuskuren da was u abokan aikinsu sukayi na harbi yayin atisaye da horon da sukeyi.

Hukumar sojin sojinNajeriya ta bayyana wannan labari ne a shafin sada ra’ayi da zumuntarta na Tuwita a daren jiya Laraba, 20 ga watan Satumba 2018.

Jawabin yace: “ Harbin kure ya sabbaba mutuwar sojoji 2. Muna nadamar sanar da mutuwar jami’an soji biyu na rundunar 192 Battalion sakamakon harbin kuskure da aka samu a atisayen yau.”

Babban hafsan sojin Najeriya ya umurci kwamandan rundunar 26 birged Gwoza ya nada kwamiti da wur-wuri domin bincike kan ainihin abinda ya faru.”

KU KARANTA: Boka da wasu mutane biyu sun cizge idanuwan dan sanda domin tsubbu, an damke a jihar Katsina

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Hukumar sojin Najeriya ta ce zata shirya kotun soji GCM domin gurfanar da jami’an sojin da suka gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Maidugri, jihar Borno, makonni biyu da suka gabata.

Wannan sanarwa ya biyo bayan gargadin da hukumar sojin tayi cewa ba za ta lamunci rashin da’a da tarbiyya daga jami’anta da hafsoshinta ba ko ma me ya faru. Saboda haka ya saba dokoki da ka’idar gidan Soja kuma duk wanda aka kama da hakan zai fuskanci fushi doka.

Ta bayyana hakan ga sojin musamman masu yaki da ta’addanci a Arewa masa gabashin Najeriya.

Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Abbah Dikko, ya sanar da wannan gargadi ne yayinda kaddamar da cibiyar soji a Maiduguri karshen makon da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel