Tinubu, APC, na kokari tursasa Ambode janyewa daga takarar gwamnan jihar Legas

Tinubu, APC, na kokari tursasa Ambode janyewa daga takarar gwamnan jihar Legas

Rikicin siyasan da ya kunno wuta a cikin jam’iyyar APC na jihar ya dau sabon salo a jiya laraba yayinda shugabannin jam’iyyar suke kokarin tursasa gwamnan jihar janyewa daga sake takara domin tazarce.

Kana suna kokarin tilastashi ya maragoyon bayansa ga wanda shugabannin jam’iyyar ke so, Babajide Sanwo-Olu, domin maye gurbinda.

Sanwo-Olu ya zama abin fadi a siyasar jihar Legas ne lokacin da ya siya takardan takaran kujeran gwamnan jihar ranan Talatan da ya gabata, kuma ya samu goyon bayan kungiyar Tinubu.

Shugabannin kananan hukumomi 57 na jihar sun nuna goyon bayansu ga Babajide Sanwo-Olu.

Tinubu, APC, na kokari tursasa Ambode janyew daga takarar gwamnan jihar Legas

Tinubu, APC, na kokari tursasa Ambode janyew daga takarar gwamnan jihar Legas
Source: Twitter

Gwaman jihar Legas, Akinwumi Ambode da Tinubu sun kasance cikin takon tsaka wanda ya sa Tinubu ya janye goyon bayansa ga kokarin tazarcen Ambode duk da kokarin da shugabanni a fadin kasa sukayi kokarin yi.

A ranan Lahadi, uwargidan gwamnan jihar Bolanle Ambode ta ziyarci Tinubu domin rokansa ya goyi bayan mijinta amma Tinubu ya lashi takobin ba zai kara goyon bayan mijinta ba.

KU KARANTA: Rikici ya barke yayin muzaharar Ashura a Zaria, an harbi mutum daya

Majiya ta samu rahoton cewa shugabannin jam’iyyar APC ta kasa da jihar Legas sun gana ranan Laraba domin tilasta Ambode hakura da kujeran.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari yayi kokarin sanya baki cikin wanna takun tsaka tsakain Tinubu da yarinsa amma da alamun ba’a samu nasara ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel