Zaben Osun: Babu shakka zanyi rawa har zuwa gidan gwamnati – Adeleke ya mayar da martani ga APC

Zaben Osun: Babu shakka zanyi rawa har zuwa gidan gwamnati – Adeleke ya mayar da martani ga APC

- Dan takarar kujeran gwamnan jihar Osun karkashin jam’iyyar PDP ya caccaki gwamnatin APC

- Yace yana da tabbacin shine zai lashe zaben da za'ayi a ranar Asabar mai zuwa

- Adeleke ya ce zai yi rawa har zuwa gidan gwamnati bayan lashe zabe

Dan takarar kujeran gwamnan jihar Osun karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaben ranar Asabar 22 ga watan Satumba da za’a gudanar, Sanata Ademola Adeleke yace yana da tabbacin lashe zaben.

Adeleke ya bayyana hakan a taron da kungiyar matasan Oduduwa mai suna Oduduwa Youth Development Initiative suka shirya a ranar Laraba, 19 ga watan Satumba.

Zaben Osun: Babu shakka zanyi rawa har zuwa gidan gwamnati – Adeleke ya mayar da martani ga APC

Zaben Osun: Babu shakka zanyi rawa har zuwa gidan gwamnati – Adeleke ya mayar da martani ga APC
Source: Depositphotos

“Babu shakka zan yi rawa zuwa gidan gwamnati ta hanyar lashe dukkanin kananan hukumomi a jihar IOsun a ranar Asabar.

“An sanya mun suna ‘sanata mai rawa’amma kada a yi amfani da wannan wajen bata mun kima saboda kowa na rawa. Shin kun taba ganin wanda baya rawa,” inji shi.

Adeleke ya kara da cewa soyayyar da yake yiwa rawa a lokacin kuruciya ne da yake makaranta lokacin da yake zuwa gasar rawa.

KU KARANTA KUMA: Zainab Ahmed ministar kudi ce – Fadar shugaban kasa

Sanata Adeleke ya kuma caccaki gwamnatin All Progressives Congress (APC) a jihar. Yace duk wanda yaki biyan ma’aikatansa mugu ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel