'Yan Arewa ba su da wata fargaba kan sauya fasalin kasa - Makarfi

'Yan Arewa ba su da wata fargaba kan sauya fasalin kasa - Makarfi

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa kuma manemin takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar, Sanata Ahmed Makarfi, ya musanta zargin cewa 'yan Arewa na da fargaba kan sauya fasalin kasar nan da yi ma ta garambawul.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Makarfi ya bayyana cewa wannan zargi ya bayu ne bisa ga rashin aminci da yarda ta bangaren wasu 'yar Arewa masu da'awar sauya fasalin kasar nan.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa, akwai muhimmiyar bukata ta gudanar da dogon nazari kan batutuwa da tsare-tsaren sauya fasalin kasar nan domin tabbatar da adalci yayin raba duk wasu albarkatu da arzikin ƙasar bisa turba ta dace.

'Yan Arewa ba su da wata fargaba kan sauya fasalin kasa - Makarfi

'Yan Arewa ba su da wata fargaba kan sauya fasalin kasa - Makarfi
Source: Twitter

Ire-iren wannan nazari kamar yadda tsohon gwamnan ya bayyana sun hadar da waiwaye bisa ga bincike da tsare-tsarem sauya fasalin kasa da za su kawo karshen barazanar tsaro da kasar nan take fuskanta a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Har yanzu ina bayan Atiku - Wani jigo na jam'iyyar APC, Kwande

Makarfi ya kara da cewa, ana ci gaba da zargin 'yan Arewa da fargabar sauya fasalin kasar nan sakamakon da'awar sauya fasalin da wasu shugabannin yankin ke yi da ba su da wata manufa da kidiri da ya wuce na soyuwar zukatan su.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na daya daga cikin shugabannin kasashen duniya 88 da za su gabatar da jawabai yayin taron majalisar dinkin duniya da za a gudanar a kasar Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel