Zaben Osun: Jam’iyyar PDP ta maidawa APC kakkausan raddi

Zaben Osun: Jam’iyyar PDP ta maidawa APC kakkausan raddi

Labari ya kai gare mu cewa babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta maidawa Takwarar ta APC martani na sukar ‘Dan takarar ta da tayi a zaben sabon Gwamnan Jihar Osun da za ayi kwanan nan.

Zaben Osun: Jam’iyyar PDP ta maidawa APC kakkausan raddi

Gbenga Oyetola na APC zai kara da Ademola Adeleke
Source: Depositphotos

A shekaran jiya ne Shugaban kasa Buhari da Jagororin Jam’iyyar APC su ka leka Jihar Osun domin yi wa ‘Dan takarar Jam’iyyar kamfe. A nan ne Shugaban APC na kasa Adams Oshiomhole ya soki ‘Dan takarar da PDP ta tsaida.

Shugabannin PDP irin su Uche Secondus, Atiku Abubakar da Bukola Saraki sun shiga Jihar Osun domin taya ‘Dan takarar Jam’iyyar yakin neman zaben da za ayi kwanan nan inda su kayi wa Jam’iyyar APC raddi na kalaman ta.

Bukola Saraki ya fadawa Jama’a su yi watsi da abin da ‘Yan APC su ka fada masu. Shugaban APC dai ya nemi jama’a su guji ‘Dan takarar PDP Nuruddeen Ademola Adeleke domin bai san komai a aikin Gwamnati ba sai tika rawar disko.

KU KARANTA: APC: Oshiomhole da gwamnonin APC sun saka labule

Adams Oshiomhole ya nemi Jama’an Osun su zabi wanda ya ke da gogewa wajen fahimtar tattalin arziki ne da kuma sanin aiki. Sai dai Saraki yace babu wata kwarewa wajen wadanda ba su biyan albashin Ma’aikata na tsawon lokaci.

Shugaban Majalisar Dattawan dai yayi tir da Gwamnatin APC a Jihar Osun wanda tayi shekaru 3 tana biyan wasu Ma’aikatan Jihar gutsurarren albashi. Saraki yayi kira ga Mutanen Jihar su yi waje da Gwamnatin APC a zaben da za ayi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa mutanen Jihar Osun cewa dole APC ta cigaba da rike Jihar lokacin da ya shiga Kamfe a makon nan. Gbenga Oyetola dai zai yi takara ne da Sanatan na Osun ta Yamma Ademola Adeleke.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel