Kungiyar kwadago ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ko ta shiga yajin aiki

Kungiyar kwadago ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ko ta shiga yajin aiki

- Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta ce zata shiga yajin aiki nan da 26 ga watan Satumba

- Yajin aiki wanda zai kasance na sai-baba-ta-gani zai shafi kungiyoyin fararen hula

- NLC ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 don cika alkawarinta na karin albashi

Bisa ga dukkan alamu, gazawar gwamnatin tarayya na yanke kyakkyawan hukunci akan karin albashi mafi karanci, zai tilastawa mambobin kungiyar kwadago ta kasa NLC shiga yajin aiki a fadin kasar a ranar 26 ga watan Satumba.

Yajin aiki wanda zai kasance na sai-baba-ta-gani zai shafi kungiyoyin fararen hula.

AWanna tattara wannan rahoton ne bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kungiyar NLC da ya gudana a Abuja, ranar Laraba.

Kungiyar kwadago ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ko ta shiga yajin aiki

Kungiyar kwadago ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 ko ta shiga yajin aiki
Source: Depositphotos

Ayuba Wabba, shugaban NLC na kasa wanda ya karanta jawabin bayan taro inda ya ke bayyana matsayarsu, ya kuma bayyana damuwarsa dangane da irin halin ko in kula da kwamitin karin albashi mafi karanci daga gwamnatin tarayya ya nuna, na dage zamanta, wanda ake sa ran zata kammala aikinta a wannan zaman.

KARANTA WANNAN: Ambaliyar ruwa ta cinye wata karamar hukuma a jihar Jigawa

"Majalisar zartaswa ta NLC ta fuskanci wannan dage zaman da kwamitin ya yi, ya saba da koyarwar da ke cikin tsari na 98 da 131 na kwadago."

Jawabin bayan taro ya bayyana cewa NLC ta baiwa gwamnatin tarayya wa'adin kwanaki 14 don cika alkawarinta na karin albashi, wanda gaza yin hakan, zai tilasta kungiyar kwadago dama na faraeen hula shiga yajin aikin sai-baba-ta-gani.

"Majalisar zartaswa ta NLC ta yanke hukuncin cewa dukkanin kungiyoyin kwadago dana fararen hula da ke jihohi 36 tare da na birnin tarayya Abuja, za su bi umarnin NEC na jagorantar mambibinsu shiga yajin aiki da zaran NEC ta bayar da umarnin hakan" a cewar jawabin bayan taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel