Tsautsayi ya fada wa Soji biyu a wasan bindiga kuma sun mutu

Tsautsayi ya fada wa Soji biyu a wasan bindiga kuma sun mutu

Wasu dakarun soji biyu da ke bataliyar 192 sun rasu sakamakon harba bindiga da wani sojin yayi cikin kuskure yayin da sojojin ke wani atsaye.

Lamarin ya faru ne a jiya Laraba 19 ga watan Satumban 2018.

Kamar yadda Hukumar Sojin ta bayyana a shafinta na Twitter, Shugaban Hafsin Sojin Najeriya, Laftanant Janar Tukur Buratai ya umurci a kafa kwamiti da za ta gudanar da bincike kan afkuwar lamarin.

Kazalika, wasu jami'an kwalejin tsaro na kasa da ke Abuja sun samu horaswa daga kwararu na Kwalejin Kasa da Kasa ta Harkokin Tsaro da ke Washington na Amurka. An basu horon ne domin taimaka musu wajen yaki da ta'addanci musamman Boko Haram.

NAJI.com ta gano cewa kwamandan NDC, Edward Yeibo ya ce an bayar da horon ne domin inganta kwarewar sojin musamman wajen yaki da Boko Haram tare da musayar ilimi tsakanin Sojin Najeriya da na Amurka.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel