Har yanzu ina bayan Atiku - Wani jigo na jam'iyyar APC, Kwande

Har yanzu ina bayan Atiku - Wani jigo na jam'iyyar APC, Kwande

Wani tsohon jakadan Najeriya zuwa kasar Switzerland kuma daya daga cikin jiga-jigan da suka assasa jam'iyyar APC, Ambasada Yahaya Kwande, ya bayyana cewa har ila yau yana nan akan bakansa na ci gaba da goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Ambasada Kwande ya kuma bayyana cewa, ya halarci wani yawon shawagi da taron gangami na yakin neman zaben Atiku, manemin takarar kujerar shugaban kasa a jam'iyyar PDP domin tabbatar da biyayyarsa a gare shi da kuma goyon baya.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, Atiku ya ziyarci birnin Jos na jihar Filato domin neman amincin wakilan jam'iyyar sa ta PDP yayin da zaben fidda gwani ke ci gaba da karatowa.

Har yanzu ina bayan Atiku - Wani jigo na jam'iyyar APC, Kwande

Har yanzu ina bayan Atiku - Wani jigo na jam'iyyar APC, Kwande
Source: Depositphotos

A yayin jawabansa ga mambobi a shelkwatar jam'iyyar dake birnin Jos, Kwande ya bayyana cewa, bai taba tsintar kansa cikin wannan yanayi na siyasa ba, inda yake shaukin ganin Atiku ya kasance shugaban kasar nan ta Najeriya.

KARANTA KUMA: PDP tayi kira kan kawo karshen shugabancin APC a jihar Osun

Kwande ya kuma kara da cewa, duk da kasancewarsa dan jam'iyyar APC, ba ya da wani mafificin zabi cikin manema takarar shugaban kasar nan da ya wuce Atiku kasancewarsa mafi cancantar jagoranci a cikin su.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Atiku da Saraki sun yi kira kan kawo karshen shugabancin jam'iyyar APC a jihar Osun yayin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a karshen wannan mako.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel